Abun lura...
Duk da maƙudan kuɗaɗe da turawa suke bawa Shugabanninmu na Demokraɗiyya a Nijer don daƙile kwararowar ƴan cirani, wannan bai hana ƴan ciranin tafiya daga ƙasashen daban-daban ba. Sai dai su karɓe kuɗin da suka yi bara ka rasa in da su ka sa su, amma kaga ƴan ciranin suna tafiya ba dare ba rana.
Ko ba komi wannan dokar ta jawo mana baƙin jini, saboda ta kansa ana muzgunawa masu zuwa cirani, wasu a hana su, wasu kuma cin hanci suke bawa jami'a tsaron kan hanya kuma sai su bari su wuce. Ga duk ɗan Nijer da yake zama Senegal, ko Gambia ko wasu ƙasashe da waɗannan ƴan ciranin ke yawan tafiya wani lokaci za kaji suna faɗin maganganu marasa daɗi ga ƙasarmu Nijer ko su ce jami'anmu basu da tausayi, ko kuma an karɓe kudinsu, ko an musu Tara, ko wani abo da zai sa su ji, sun tsani ƙasar. kuma yawanci hakan na faruwa ne, dalilin irin waɗannan dokokin masu hana zirga-zirga wannan yankin.
Allah ya Kyauta.
Allah ya zaunar damu lafiya.
Comments
Post a Comment