MENE NE MARGIN TRADING (1)
Margin Trading dai tsari ne na aiwatar da cinikayyar kaddarorin kudi "financial instruments" ta hanyar amfani da kudaden da wasu manyan diloli su ka samar. Idan mu ka kwatanta da game-garin taskokin cinikayya "trading account", za mu ga cewa taskokin mu'amala da tsarin cinikayyar margin "margin trading account" na ba mutane damar yin mu'amala da manyan kudade "greater capital" na rance domin bude ciniki.
Wannan salo na margin na habaka sakamakon kasuwanci ta yadda 'yan kasuwa ke iya ganin gagarumar riba ga duk kasuwancin da ya faru cikin nasara. Wannan dama ta fadada sakamakon kasuwanci ita ce sanadiyyar shaharar wannan tsari hatta a kasuwanni irin su Foreign Exchange. Har wa yau, ana dai amfani da margin a kasuwannin hannun jari da ake kira 'stock exchange', kasuwar kirifto da sauran su.
A kasuwannin mu na al'ada "traditional markets", galibi kudin da ka ke ranta ka shiga kasuwa da su, manyan diloli masu zuba jari ne su ka samar da su "investment brokers". A kasuwar kirifto kuma, 'yan kasuwa ne "traders" ke samar da wadannan kudade, da su ke samun kudin ruwa "interest" a bisa girman bukatar kasuwa ta ire-iren wadannan kudade na su. Koda yake, wasu daga cikin dandalin da ake cinikayyar kudaden na kirifto "crypto exchange" na samar da wadannan kudade na rance ga masu mu'amala su ma.
Shamsudin Yashe ✍
Insha Allahu, zan ci gaba...
Comments
Post a Comment