Hausa Novel |||. INA DA SAMARI A SOCIAL MEDIA TUN KAFIN NAYI AURE


 INA DA SAMARI A SOCIAL MEDIA TUN KAFIN NAYI AURE


Yanzu kuma na yi aure wasu daga cikinsu sun san na yi amma da yawansu basu san na yi auren ba, kuma har yanzu ba bu abinda yasauya na mu'amilar soyayya tsakani na da su, matsalar ita ce na ka sa kaurace musu ko na yi blocked dinsu na huta saboda na shaku da su ne over .


Idan miji na yatambaye ni me nakeyi me da waya haka sai nace masa: Ai da kawaye na ne muke tattaunawa irin harkarmu ta mata. 


Ashe acikin samarin nawa akwai Miji na acikinsu wanda bai san da Ni yake chatting ba, ni ma ban gane shi ba Saboda duk ba sunayen mu na ainihi muke amfani da su a Social media ba, Kuma duk na ki bari na baiwa kowa lambar waya ta balle mu hadu a WhatsApp ko kira yashiga tsananinmu a gane ni da wuri shiyasa ma bai gane ni ba tun farko.


Sai Yanzu nake gane ai miji na ne, a karshe dai shima yagane ai da ni matarsa yake yin irin wannan chatting din haka, kuma ya tabbatar min cewa ya san ba da shi kaΙ—ai nake yin chatting din ba , yanzu zargi na yake yi dam bai yarda da ni ba, yaranmu 2 da shi ga wani cikin kuma watansa 5, duk ya ce bai yarda da su ba dole sai an je anyi gwajin jini a asibiti tukunna.


Gani ga wane.....


ALLAH ya kyauta kuma yakara tsare mana imaninmu,

Yanzu inq amfanin badi babu rai, da ace kina yin auren nan duk ki ajiye ko wanne saurayi da kikasan kuna soyayya da shi Saboda mace dai miji 1 tal take aura,


Qirqirarrar Fadakarwa ce daga dan uwanku :

✍🏻 *Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)*

Comments