SO SANADI
Shimfiɗa
Sarki Muhammadu ɗan Sabaiki, sarki ne mai ƙarfin dakaru da askarawa, ga kuma tarin dukiya sai ka ce ƙasa. Babu abin da sarkin nan ya fi sha'awa a rayuwarsa irin ya ji labarai da hikayoyi waɗanda bai taɓa jin irinsu ba. Idan aka ba shi labarin da bai taɓa ji ba, kuma har labarin ya ƙayatar da shi, to idan ya rufe mai labarin da kyauta sai ya kasa godiya.
Ana nan sai Sarki ya ji labarin wani baƙon tajirin falke, mai bayar da labarai da ake kira Hassan, ya sauka ƙasarsa. Nan da nan ya aika ya zo. Da tajiri ya zo gaban Sarki sai ya ce masa, "ina so ka ba ni labari wanda ban taɓa jin irinsa ba, idan ya ƙayatar da ni zan yi maka goma ta arziki, idan kuwa ka kasa in yi maka goma ta zagi."
Tajiri ya duƙar da kai ya ce, "Allah ya ba ka nasara, na ji na ɗauka, amma ka jinkirta mini nan da shekara guda, ni kuwa zan zo maka da labarin da, da ɗai, wani tamkarka bai taɓa jin irinsa ba."
Sarki ya ce, "tashi tafi, kada ka dawo gare ni sai bayan shekara guda."
Da tajiri ya koma gida, sai ya kira wasu amintattun bayinsa, su biyar, ya aika su cikin duniya, ya ce musu, "ku tafi cikin duniya ku nemo mini hikaya kaza," ya faɗa musu sunan hikayar. Ya ci gaba da cewa, "duk mutumin da kuka samu wannan hikaya, ku yi ƙoƙari ku rubuto mini ita, ko da mai hikayar ya nemi dinari dubu ne, to ku ba shi, ya ba ku hikayar. Ku tafi na ba ku watanni goma ku dawo." Ya kawo guzuri ya ba su.
Bayi suka watsu cikin duniya, wani ya yi Gabas, wani Yamma, wani Kudu, wani Arewa, tsawon watanni goma. Huɗu suka dawo hannu wofi. Tajiri ya yi kamar ya kashe kansa don baƙin ciki.
Shi kuwa bawa na biyar, bayan ya gama yawo bai samu abin kamawa ba, sai ya juyo zuwa gida. Bisa hanyarsa ta dawowa ya yada zango a birnin Dimashƙa. Ran nan da safe ya fito ƙofar gidan baƙin da ya sauka, sai ya ga wani saurayi yana sauri zai tafi wani wuri, har yana haɗawa da gudu-gudu. Bawa ya cim masa ya tambaye shi, "ina za ka kake sauri haka."
Saurayi ya ce, "hala kai baƙo ne? Za ni wurin dattijon da yake ba da labarai ne, duk rana irin ta yau. Ina sauri ne domin na samu wurin zama a gaba, kafin mutane su cika wurin."
Bawa ya ce, "mu tafi, ni ma ina da sha'awar jin labarai." Da ma za ni ce ta tarar da mu je mu, yaƙin ruwa ya tarar da sakaina. Suka rankaya sai wurin dattijo. Suka samu wuri suka harɗe. Da jama'a ta cika tinjim, dattijo ya shiga bayar da labarai iri-iri. Da ya gama, mutane suka yi masa kyaututtuka suka watse.
Bayan mutane sun fashe, sai bawa ya matsa wurin dattijo ya tambaye shi, "Baba, ko ka san hikaya kaza?" Ya faɗa masa sunan hikayar da ya fito nema.
Dattijo ya dube shi cike da mamaki, sannan ya tambaye shi, "kai kuwa ina ka taɓa jin sunan wannan hikaya?"
Bawa ya duƙa ya kwance wa dattijo bakin jaka, bisa ga abin da ya fito nema, ga shi har zai koma gida bai samu ba.
Dattijo ya ce, "ka yi murna, ya kai ɗana, domin kuwa daminka ya tsinke gindin kaba. Haƙiƙa na san hikayar da ka fito nema. Hikaya ce da ban taɓa zanta ta bisa hanya ba. Ba kowa ake labartawa wannan hikaya ba face sarakuna da manyan mutane da masu ilmi da masu hankali. Ka zo gobe gidana, da ke unguwa kaza, zan ba ka wannan hikaya bisa ga wasu sharuɗɗa da zan gindaya maka idan ka yarda."
Bawa ya ce, "to."
Kashegari ya samu dattijo gida ya ce, "ga ni na zo."
Dattijo ya ce, "to madalla. Da farko dai sai ka ba ni dinari ɗari, domin ita wannan hikaya ba a bayar da ita kyauta."
Nan take bawa ya ƙirgo dinari ɗari daga cikin lalitarsa ya ba dattijo. Bayan dattijo ya karɓi kuɗi sai ya ce, "to ga sauran sharuɗɗan da zan gaya maka. Ita dai wannan hikaya ba a labarta ta ga hanya, ba a faɗa wa yara, waɗanda ba su mallaki hankalinsu ba, ba a faɗa wa wawaye da jahilai. Ana labarta ta ne kawai ga sarakuna da manyan mutane da masu ilmi, da kuma masu hankali. Idan ka yarda in ba ka."
Bawa ya ce, "na yarda."
Dattijo ya ɗauko alƙalami da takarda ya ba shi, ya ce, "to rubuta abin da zan gaya maka." Ya kwashe hikayar nan ram ya faɗa masa, ya kuma ce ya karanta ya ji, idan ya rubuta daidai. Da Bawa ya karanta, dattijo ya ji babu kuskure, sai ya sallame shi ya tafi.
Washegari Bawa ya naɗe kayansa ya nufi ƙasarsu. Kwanci tashi, bayan wata biyu, ya isa gida. Ya faɗa wa maigidansa cewa buƙata ta biya. Tajiri ya karɓi labari ya karanta, sannan ya sake rubuta shi da hannunsa, ya ɗauka sai gidan Sarki.
Da zuwa ya faɗi ya yi gaisuwa, sannan ya ce, "Allah ya taimake ka, ga labarin da na yi alkawari zan kawo maka, shekara guda da ta wuce."
Sarki ya ce, "to, ina jin ka."
Tajiri ya karanta wa Sarki hikaya, tun daga farko har ƙarshe. Yayin da Sarki ya ji wannan hikaya, sai ya cika da farin ciki, ya cire rawaninsa ya naɗa wa tajiri. Ya kuma shiga gida ya tuɓe tufafinsa ya kawo masa. Ya yi masa kyuata mai yawa wadda ba ta misaltuwa, don daɗin wannan hikaya. Ya sa aka sake rubuta masa ita a cikin littafi da tawadar ruwan zinariya. Duk sadda ya yi sha'awa sai ya ɗauko littafin ya karanta. Idan ya karanta hikayar nan kuwa zai yi ta raba wa talakawansa dukiya cikin farin ciki da annushuwa saboda daɗin hikayar nan.
To, wannan hikaya ce zan fara kawo muku, ranar Laraba mai zuwa, in sha Allah. To, sai dai a cikin sharuɗɗan wannan hikaya ba a bayar da ita kyauta don daɗinta, kamar yadda dattijo ya ce. Don haka kyautar me kuka yi mini tanadi kafin na fara? 😄
Comments
Post a Comment