SHUGABAN IZALA YA MAGANTU
Shugaban Kungiyar Izala na duniya Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau yayi kira ga Shugabannin darikun sufaye da duk wanda abin ya shafe dangane da bayyanar wasu mulhidai 'yan hakika a cikin Darikar Tijjaniyyah, wanda suke cewa komai Allah ne wai babu asalin Allah sai Shehu Barhama Inyass
Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau yace dole Malaman darika su fito suyi magana indai sun tabbatar wannan akidar ba haka yake a cikin Darikar Tijjani ba, to a tashi tsaye a yaki wadannan zindikai kafin masifa da bala'i su sauka a Kasarmu Nigeria
Dukkan Musulmi su zama shaida, Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a madadin Ahlussunnah na Nigeria, saura wadanda abin ya shafa
Muna fatan kada Allah Ya jarrabemu bisa laifin da wawayen cikin mu suke aikawata
Comments
Post a Comment