Buri na makarantar fim da na kafa ta zama jami’a – Hamisu Iyantama
A wata hira da fitattaccen furodusa, kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Alhaji Hamisu Lamido Iyantama yayi da Fim Magazine a Oktoba 2015 ya bayyana cewa ya gina makaranta da zata riƙa bada horo a fannin koyon fim, aikin jarida, aikin talbijin da kuma wasu kwasa-kwasai na musamman da suka shafi harkar yaɗa labarai. Makarantar zata riƙa bayar da takardar diploma, advanced diploma, da kuma shaidar kwarewa a wasu kwasa-kwasai.
Hakan ya faru ne a yunkurin sa na ganin ya bada gudunmawa wajen cike giɓin da ake dashi ta fannin kwarewa a wadannan fannoni, musamman a arewa, domin jama’ar wannan yanki namu su amfana,kuma a samu kwararrun da zasu yi gogayya da sauran mutane na duniya a fannin fim, talbijin da aikin jarida.
A wata hirar da suka sake yi dashi a Mujallar ta ranar 20/11/2023 ya kara da cewa
“…..makaranta ce ka sani na gina, ina son ta fara aiki, amma waɗanda za su saka hannun jari na ke nema su shigo ciki domin abin ya fi haka girma don ta zama kamar wata jami’a, ba yadda ni na ɗauko shi da farko ba”.
To ina masu son zuba jari a wannan makaranta, ga dama ta samu, domin a bunkasa wannan harka ta fim, da sauran abubuwa da suka shafi yada labarai.
#iyantama #fim #kannywood

Comments
Post a Comment