Labaran Siyasa || Siyasar Kano Sai Kano. GWAMNAN KANO ABBA YANA CIKIN TSAKA MAI WUYA


 GWAMNAN KANO ABBA YANA CIKIN TSAKA MAI WUYA


Yanzu nake karanta labarin wasu 'yan kasuwa a Kano sun sake kai karan Maigirma Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zuwa gaban majalisar dinkin duniya reshen Nigeria, suna zarginsa da ruguza dukiyarsu da yayi


Jama'a kun fahimci abinda hakan ke nufi kuwa? idan korafin nasu ya karbu to idan Abba ya bar kujeran Gwamna da wahala ya samu mafaka a Kasar waje, domin suna da ajandar kamashi da zaran sun kwace kujeran, a fahimtata wannan shine dalilin da yasa suka kai karansa gaban majalisar dinkin duniya don a hanashi asylum 


Bayan wannan, ku sani cewa akwai hukuncin Kotu a kansa na ya biya wasu 'yan kasuwar Filin idi da ya rushe musu dukiya diyya na sama da Naira Biliyan 30 idan ban manta adadin kudin ba, ya kuke tunanin zai kasance idan suka kwace kujeran bai biya diyyar ba? ba zasu barshi ba


A doka duk wani Gwamna da yake fuskantar shari'ah a Kotu akan nasaran kujeransa to ba za'a sakar masa cikakken iko da asusun Gwamnatin jihar ba har sai an kammala shari'ah, to kun ga babu kudin da zai biya wannan diyyar


Allah shaida ne, ba fata nake masa ba, amma ku rubuta ku ajiye watakila Abba daga gidan Gwamnati sai gidan yari, sai dai addu'ah tana iya canza girman kaddara


Babban illar da Abba ya yiwa kansa shine ruguza dukiyar mutane da yayi wanda bana shakka Kwankwaso ne ya sa akayi, domin na ga bidiyon Kwankwaso yana jawabi yana cewa ai sun yiwa mutane gargadi, duk wanda ya gina gida a filayen Gwamnati da Ganduje ya sayar to ginin ko ya kai hawan bene dubu sai sun rushe


Don haka duk wulakancin da mutanen Abuja zasu yiwa Abba Kwankwaso ne ya jawo masa


Kamar yadda nace addu'ah tana iya canza tasirin kaddara, don haka magoya bayan Abba tsinuwa da zagi ba shine mafita a gareku da Gwamnanku ba, babu abinda yake bukata a yanzu daga gareku face addu'ah na Allah Ya tabbatar masa da kujeransa 


Muna fatan Allah Ya bashi mafita na alheri

Comments