Nishadi ||. ALAKARMU DA MATA SAI HAKURI


 ALAKARMU DA MATA SAI HAKURI


A wani lokaci idan matarka ta bata maka rai sai kaji rayuwar ma gaba daya ta fita a ranka, ko kaji cewa babu amfani cigaba da zama da mata, sai kaji kana son rayuwar kadaici


Idan kayi fushi ka kaurace mata, ta dena ganinka, kaki cin abincinta, kaki kwana a dakinta sai tafi kowa shiga damuwa


Matana ta taba bata min rai, da tsakar dare na fita daga gidan na shiga mota zan kwana a cikin mota, na kai kusan mintuna 25 a cikin mota ana zabga ruwan sama, tayi ta kirana a waya naki dauka, haka a cikin ruwan ta fito ta tsaya a gaban motan ruwan yana dukanta 


Daga karshe ta ban tausayi na bude motar ta shigo muka sasanta a cikin mota, ta ban hakuri kuma nima na hakura


Magana ta gaskiya na miji duk gatansa duk arzikinsa duk girman rawanin sarautarsa da duk abinda yake takama da shi a duniya bai taba samun nutsuwa sai da mace a kusa da shi, kuma sai ya durkusa wa mace ya nemi alfarmata, hatta Sarkin Yanka idan aka shiga other room sai ya rusuna wa mace


Haka nan mace, duk abinda take takama da shi a duniya ba zata taba rayuwa cikin nutsuwa ta hakika ba idan babu miji a tare da ita, namiji shine gatanta, shine rufin asirinta kuma shine mutuncinta


Gaskiya duk macen da ta haura shekaru 30 matukar bata da miji to ba a cikin hayyacinta take ba, idan ba zaman kanta take ba kuma bata sana'a ko aiki, takaicin sayan sanitary pad kadai ya isheta damuwa, saboda iyayenta ba zasu ji da damuwarta ba sai na kannenta


Maza mu cigaba da hakuri da matan mu, Zuciyar mata kamar hawainiya suke wajen rikidewa musamman idan Allah Ya jarrabeka da mace mai zafin kishi, kuma matan da basa shan wahala a gidan miji zaku ga sune suka fi wahalar da mazajensu


Mata masu kananun shekaru wadanda basu goge da rayuwar zaman gidan miji ba sun fi wahalar da na miji, idan ta takaleka kar ka tanka, kawai ka fice mata daga gidan, kaki cin abincinta hakan yafi saurin ladabtar dasu, amma idan kace zaka tanka to abinda ake ki ne zai iya faruwa


Sannan idan matarka tana wahalar da kai bata baka kulawan da ya dace, to ina baka shawara ka kara aure, ka fara laluben wata bazawara wanda ta haura 40yrs wanda ta goge da rayuwa domin ta dauke maka kewa


Muna fatan Allah Ya kara mana hakuri da juna

Comments